Ezekiel 7
World English Bible (en) → Hausa Open Bible (Biblica) (ha)
- 1
Maganar Ubangiji ta zo gare ni cewa,
- 2
“Ɗan mutum, ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yake cewa wa ƙasar Isra’ila, “ ‘Ƙarshe ya zo! Ƙarshe ya zo a kan kusurwoyi huɗu na ƙasar.
- 3
Ƙarshe yanzu yana a kanki. Zan fashe fushina a kanki. Zan shari’anta ki bisa ga halinki in sāka miki kuma saboda dukan ayyukan banƙyamar da kika yi.
- 4
Ba zan dube ki da tausayi; ko in ƙyale ki ba. Tabbatacce zan sāka miki saboda halinki da kuma ayyukanki masu banƙyama a cikinki.
- 5
“Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “ ‘Masifa! Masifar da ba a taɓa gani ba tana zuwa.
- 6
Ƙarshe ya zo! Ƙarshe ya zo! Ya farka a kanki. Ga shi, ya zo!
- 7
Ƙaddara ta auko miki, ya ke wadda ke zama cikin ƙasar. Lokaci ya yi, rana ta gabato; akwai fargaba, ba farin ciki ba, a kan duwatsu.
- 8
Ina gab da fasa hasalata a kanki in kuma aukar da fushina a kanki; zan shari’anta ke bisa ga halinki in kuma sāka miki saboda dukan ayyukanki masu banƙyama.
- 9
Ba zan dube ki da tausayi ko in ƙyale ke ba; zan sāka miki bisa ga halinki da kuma ayyukan masu banƙyama a cikinki.
- 10
“ ‘Ga shi ranar ta zo! Ta iso! Ƙaddararki ta keto, sandar ta yi toho, girman kai ya yi fure!
- 11
Rikici ya yi girma ya zama sandar da za a hukunta mugunta; babu wani daga cikin mutanen da za a bari, babu wani dukiyarsu da za a bari, babu wani abin amfani.
- 12
Lokaci ya yi! Ranar ta gabato! Kada mai saya ya yi farin ciki ko kuwa mai sayarwa ya yi baƙin ciki, gama hasala tana a kan dukan jama’a.
- 13
Mai sayarwa ba zai mayar da ƙasar da ya sayar tuntuni ba muddin dukansu suna da rai, gama ba za a sauya wahayin da ya shafi dukan jama’a ba. Saboda zunubansu, babu ɗayansu da zai adana ransa.
- 14
“ ‘Ko da yake suna busa ƙaho suna kuma shirya kome, ba wanda zai tafi yaƙi, gama hasalata tana a kan dukan jama’a.
- 15
A waje takobi ne, a ciki annoba ne da yunwa; waɗanda suke fili za su mutu ta wurin takobi, waɗanda kuma suke cikin birni yunwa da annoba za su cinye su.
- 16
Duk waɗanda suka tsira suka tsere za su kasance a cikin duwatsu, suna kuka kamar kurciyoyin kwaruruka, kowanne saboda zunubansa.
- 17
Kowane hannu zai raunana, kowace gwiwa kuma za tă zama marar ƙarfi kamar ruwa.
- 18
Za su sa tufafin makoki su kuma rufu da fargaba. Fuskokinsu kuma za su rufu da kunya a kuma aske kawunansu.
- 19
“ ‘Za su zubar da azurfarsu a tituna, zinariyarsu kuma za tă zama ƙazantacciyar aba. Azurfarsu da zinariyarsu ba za su iya cetonsu a ranar hasalar Ubangiji ba. Ba za su ƙosar da yunwansu ko su cika cikinsu da shi ba, gama su ne sanadin tuntuɓensu cikin zunubi.
- 20
Sun yi fariya kyan kayan adonsu suka kuma yi amfani da su don su yi gumakansu masu banƙyama, da ƙazantattun abubuwa.
- 21
Zan ba da su duka kamar ganima ga baƙi da kuma kamar abin da aka washe ga mugayen duniya, za su kuma ƙazantar da su.
- 22
Zan juye fuskata daga gare su, za su kuwa ƙazantar da wurina mai daraja; ’yan fashi za su shiga su kuma ƙazantar da shi.
- 23
“ ‘Ka shirya sarƙoƙi, domin ƙasar ta cika da alhakin jini, birnin kuma ya cika da rikici.
- 24
Zan kawo al’ummai mafi mugunta su mallaki gidajenku; zan kawo ƙarshen fariyar masu ƙarfi, Wurare Masu Tsarkinsu za su ƙazantu.
- 25
Sa’ad da wahala ta zo, za su nemi salama, amma ba za su same ta ba.
- 26
Masifa a kan masifa za su zo, jita-jita kuma a kan jita-jita. Za su yi ƙoƙarin samun wahayi daga annabi; koyarwar doka ta wurin firist za tă ɓace, kamar yadda shawarar dattawa za tă ɓace.
- 27
Sarki zai yi makoki, yerima zai fid da zuciya, hannuwan mutanen ƙasar kuma za su yi rawa. Zan sāka musu bisa ga ayyukansu, zan kuma hukunta su bisa ga ma’auninsu.