1 Samuel 3
World English Bible (en) → Hausa Open Bible (Biblica) (ha)
- 1
Yaron nan Sama’ila ya yi hidima a gaban Ubangiji a ƙarƙashin Eli. A waɗannan kwanaki kuwa jin magana daga wurin Ubangiji ba safai ba, babu kuma wahayi da yawa.
- 2
Wata rana da dare Eli da idanunsa sun kusa makancewa har ba ya iya gani sosai yana kwance a inda ya saba.
- 3
Fitilar Allah kuwa tana ci, ba tă mutu ba tukuna, Sama’ila kuma na kwance a haikali na Ubangiji inda akwai akwatin Allah.
- 4
Sai Ubangiji ya kira Sama’ila.
- 5
Sai ya ruga wajen Eli ya ce, “Ga ni, gama ka kira ni.”
- 6
Ubangiji ya sāke kiransa ya ce, “Sama’ila!” Sama’ila ya tashi kuma ya je wurin Eli ya ce, “Ga ni, gama ka kira ni.”
- 7
Sama’ila dai bai riga ya san Ubangiji ba tukuna. Ba a kuma taɓa bayyana maganar Ubangiji a gare shi ba tukuna ba.
- 8
Ubangiji ya kira Sama’ila sau na uku, Sama’ila kuma ya tashi ya tafi wurin Eli, “Ga ni, gama ka kira ni.”
- 9
Saboda haka, Eli ya gaya wa Sama’ila cewa, “Je ka kwanta, in kuma ya kira ka, ka ce masa, ‘Ya Ubangiji ka yi magana gama bawanka yana saurara.’ ” Sama’ila ya koma ya kwanta a wurin kwanciyarsa.
- 10
Ubangiji kuma ya zo ya tsaya a wurin, yana kira ya ce, “Sama’ila, Sama’ila!” Kamar yadda ya kira a lokutan baya.
- 11
Ubangiji ya ce wa Sama’ila, “Duba ina dab da yin wani abu a Isra’ila da zai sa kunne kowa da yake ji, yă ji tsoro.
- 12
A ranar zan cika dukan maganar da na yi game da Eli da iyalinsa, daga farko har ƙarshe.
- 13
Gama na gaya masa zan hukunta gidansa har abada saboda zunubin da yake sane da shi; ’ya’yansa sun wulaƙantar da kansu, shi kuma bai tsawata musu ba.
- 14
Saboda haka na rantse a kan gidan Eli, ‘Ba za a taɓa shafe laifin gidan Eli da hadaya ko baiko ba.’ ”
- 15
Sama’ila kuwa ya kwanta har safe, sa’an nan ya buɗe ƙofofin gidan Ubangiji. Ya ji tsoro yă gaya wa Eli wahayin,
- 16
amma Eli ya kira shi ya ce, “Sama’ila, ɗana.”
- 17
Eli ya ce, mene ne ya ce maka? Kada ka ɓoye mini. Allah ya yi da kai har ma fiye in ka ɓoye mini kome da ya ce maka.
- 18
Don haka sai Sama’ila ya gaya masa kome bai ɓoye masa kome ba. Sa’an nan Eli ya ce, “Shi ne Ubangiji bari yă yi abin da ya yi kyau a gare shi.”
- 19
Ubangiji kuwa yana tare da Sama’ila har girmansa bai kuma bar ko ɗaya daga maganarsa ta kāsa cika ba.
- 20
Dukan Isra’ila daga Dan har Beyersheba suka shaida amincin Sama’ila annabi ne na Ubangiji.
- 21
Ubangiji kuwa ya dinga bayyana a Shilo, a nan ya bayyana kansa ga Sama’ila ta wurin maganarsa.