1 Chronicles 6
World English Bible (en) → Hausa Open Bible (Biblica) (ha)
- 1
’Ya’yan Lawi maza su ne,
- 2
’Ya’yan Kohat maza su ne,
- 3
Yaran Amram su ne,
- 4
Eleyazar shi ne mahaifin Finehas,
- 5
Abishuwa mahaifin Bukki,
- 6
Uzzi mahaifin Zerahiya,
- 7
Merahiyot mahaifin Amariya,
- 8
Ahitub mahaifin Zadok,
- 9
Ahimawaz mahaifin Azariya,
- 10
Yohanan mahaifin Azariya (shi ne ya yi hidima a matsayin firist a haikalin da Solomon ya gina a Urushalima),
- 11
Azariya mahaifin Amariya,
- 12
Ahitub mahaifin Zadok,
- 13
Shallum mahaifin Hilkiya,
- 14
Azariya mahaifin Serahiya,
- 15
Yehozadak ne aka ɗauka sa’ad da Ubangiji ya tura Yahuda da Urushalima zuwa zaman bauta ta hannun Nebukadnezzar.
- 16
’Ya’yan Lawi maza su ne,
- 17
Waɗannan su ne sunayen ’ya’yan Gershom.
- 18
’Ya’yan Kohat maza su ne,
- 19
’Ya’yan Merari maza su ne,
- 20
Na Gershom su ne,
- 21
Yowa,
- 22
Zuriyar Kohat su ne,
- 23
Elkana,
- 24
Tahat, Uriyel,
- 25
Zuriyar Elkana su ne,
- 26
Elkana, Zofai,
- 27
Eliyab
- 28
’Ya’yan Sama’ila maza su ne,
- 29
Zuriyar Merari su ne,
- 30
Shimeya, Haggiya
- 31
Waɗannan su ne mutanen da Dawuda ya sa su lura da waƙa a cikin gidan Ubangiji bayan da aka kawo akwatin alkawari yă huta a can.
- 32
Suka yi hidima da waƙa a gaban tabanakul, Tentin Sujada, sai da Solomon ya gina haikalin Ubangiji a Urushalima. Suka yi ayyukansu bisa ga ƙa’idodin da aka shimfiɗa musu.
- 33
Ga mutanen da suka yi hidimar, tare da ’ya’yansu maza.
- 34
ɗan Elkana, ɗan Yeroham,
- 35
ɗan Zuf, ɗan Elkana,
- 36
ɗan Elkana, ɗan Yowel,
- 37
ɗan Tahat, ɗan Assir,
- 38
ɗan Izhar, ɗan Kohat,
- 39
da kuma Asaf ’yan’uwan Heman, waɗanda suka yi hidima a hannun damansa.
- 40
ɗan Mika’ilu, ɗan Ba’asehiya,
- 41
ɗan Etni,
- 42
ɗan Etan, ɗan Zimma,
- 43
ɗan Yahat,
- 44
da kuma daga ’yan’uwansu, mutanen Merari, a hannun hagunsa.
- 45
ɗan Hashabiya,
- 46
ɗan Amzi, ɗan Bani,
- 47
ɗan Mali,
- 48
Aka ba ’yan’uwansu Lawiyawa dukan sauran ayyukan tabanakul, gidan Allah.
- 49
Amma Haruna da zuriyarsa su ne waɗanda suke miƙa hadayu a kan bagaden hadaya ta ƙonawa da kuma a kan bagaden turare haɗe da dukan abin da ake yi a Wuri Mafi Tsarki, suna yin kafara domin Isra’ila, bisa ga dukan abin da Musa bawan Allah ya umarta.
- 50
Waɗannan su ne zuriyar Haruna,
- 51
Bukki,
- 52
Merahiyot, Amariya,
- 53
Zadok
- 54
Waɗannan su ne wuraren zamansu da aka ba su rabo su zama yankunansu (aka ba wa zuriyar Haruna waɗanda suke daga gidan Kohat, domin rabo na fari nasu ne):
- 55
Aka ba su Hebron a Yahuda tare da wuraren kiwon da suke kewayenta.
- 56
Amma filaye da ƙauyukan da suke kewayen birnin aka ba wa Kaleb ɗan Yefunne.
- 57
Saboda haka aka ba wa zuriyar Haruna Hebron (birnin mafaka), da Libna, Yattir Eshtemowa,
- 58
Hilen, Debir,
- 59
Ashan, Yutta da Bet-Shemesh, tare da wuraren kiwonsu.
- 60
Daga kabilar Benyamin kuma aka ba su Gibeyon, Geba, Alemet da Anatot, tare da wuraren kiwonsu.
- 61
Aka ba sauran zuriyar Kohat rabon garuruwa goma daga gidajen rabin kabilar Manasse.
- 62
Aka ba zuriyar Gershom, gida-gida, rabon garuruwa goma sha uku daga kabilan Issakar, Asher da Naftali, da kuma daga sashen rabi kabilar Manasse da yake a Bashan.
- 63
Aka ba zuriyar Merari, gida-gida, rabon garuruwa goma sha biyu daga kabilan Ruben, Gad da Zebulun.
- 64
Saboda haka Isra’ilawa suka ba Lawiyawa waɗannan garuruwa da wuraren kiwonsu.
- 65
Daga kabilan Yahuda, Simeyon da Benyamin suka ba su rabon sunayen garuruwan da aka ambata.
- 66
Aka ba wa waɗansu na mutanen gidan Kohat yankin garuruwansu daga kabilar Efraim.
- 67
A ƙasar tudun Efraim aka ba su Shekem (birnin mafaka), da Gezer,
- 68
Yokmeyam, Bet-Horon,
- 69
Aiyalon da Gat-Rimmon, tare da wuraren kiwonsu.
- 70
Daga rabin kabilar Manasse kuwa, Isra’ilawa suka ba da Aner da Bileyam, tare da wuraren kiwonsu, ga sauran gidajen mutanen Kohat.
- 71
Mutanen Gershom suka sami waɗannan.
- 72
daga kabilar Issakar suka sami Kedesh, Daberat,
- 73
Ramot da Anem, tare da wuraren kiwonsu;
- 74
daga kabilar Asher suka sami Mashal, Abdon,
- 75
Hukok da Rehob, tare da wuraren kiwonsu;
- 76
daga kabilar Naftali kuwa suka sami Kedesh a Galili, Hammon da Kiriyatayim, tare da wuraren kiwonsu.
- 77
Mutanen Merari (sauran Lawiyawan) suka sami waɗannan.
- 78
daga kabilar Ruben a hayin Urdun a gabashi Yeriko suka sami Bezer a hamada, Yahza,
- 79
Kedemot da Mefa’at, tare da wuraren kiwonsu;
- 80
daga kabilar Gad kuwa suka sami Ramot a Gileyad, Mahanayim,
- 81
Heshbon da Yazer, tare da wuraren kiwonsu.