1 Chronicles 27
World English Bible (en) → Hausa Open Bible (Biblica) (ha)
- 1
Wannan shi ne jerin Isra’ilawa, kawunan iyalai, shugabannin dubu-dubu da shugabannin ɗari-ɗari, da manyan ma’aikatansu, waɗanda suka yi wa sarki hidima a dukan abin da ya shafi ɓangarorin mayaƙan da suke aiki wata-wata a dukan shekara. Kowane sashe yana da mutane 24,000.
- 2
Wanda yake lura da sashe na fari, na wata na farko, shi ne Yashobeyam ɗan Zabdiyel. Akwai mutane 24,000 a sashensa.
- 3
Shi zuriyar Ferez ne kuma babba na dukan shugabannin mayaƙa don wata na farko.
- 4
Wanda yake lura da sashen don wata na biyu shi ne Dodai mutumin Ahowa; Miklot ne shugaban sashensa. Akwai mutane 24,000 a sashensa.
- 5
Shugaban mayaƙa na uku, don wata na uku, shi ne Benahiya ɗan Yehohiyada firist. Shi ne babba kuma akwai mutane 24,000 a sashensa.
- 6
Wannan shi ne Benahiya wanda yake ɗaya daga cikin jarumawa Talatin nan kuma shi ne yake babba a cikin Talatin ɗin. Ɗansa Ammizabad ne yake lura da sashensa.
- 7
Na huɗu, don wata na huɗu, shi ne Asahel ɗan’uwan Yowab; ɗansa Zebadiya shi ne magājinsa. Akwai mutane 24,000 a sashensa.
- 8
Na biyar don wata na biyar, shi ne Shamhut mutumin Izhar shugaban mayaƙa. Akwai mutane 24,000 a sashensa.
- 9
Na shida, don wata na shida, shi ne Ira ɗan Ikkesh mutumin Tekowa. Akwai mutane 24,000 a sashensa.
- 10
Na Bakwai, don wata na bakwai, shi ne Helez mutumin Felon, mutumin Efraim. Akwai mutane 24,000 a sashensa.
- 11
Na takwas, don wata na takwas, shi ne Sibbekai mutumin Husha, mutumin Zera. Akwai mutane 24,000 a sashensa.
- 12
Na tara, don wata na tara, shi ne Abiyezer mutumin Anatot, mutumin Benyamin. Akwai mutane 24,000 a sashensa.
- 13
Na goma, don wata na goma, shi ne Maharai mutumin Netofa, mutumin Zera. Akwai mutane 24,000 a sashensa.
- 14
Na goma sha ɗaya, don wata goma sha ɗaya, shi ne Benahiya mutumin Firaton, mutumin Efraim. Akwai mutane 24,000 a sashensa.
- 15
Na goma sha biyu don wata goma sha biyu, shi ne Heldai mutumin Netofa, daga iyalin Otniyel. Akwai mutane 24,000 a sashensa.
- 16
Shugabannin da suke bisa kabilan Isra’ila,
- 17
bisa mutanen Lawi shi ne, Hashabiya ɗan Kemuwel;
- 18
bisa mutanen Yahuda shi ne, Elihu, ɗan’uwan Dawuda;
- 19
bisa mutanen Zebulun shi ne, Ishmahiya ɗan Obadiya;
- 20
bisa mutanen Efraim shi ne, Hosheya ɗan Azaziya;
- 21
bisa ɗayan rabi kabilar Manasse a Gileyad shi ne, Iddo ɗan Zakariya;
- 22
bisa mutanen Dan shi ne, Azarel ɗan Yeroham.
- 23
Dawuda bai ƙirga mutanen da suke ’yan shekara ashirin ko ƙasa ba, domin Ubangiji ya yi alkawari zai sa Isra’ila su yi yawa kamar taurari a sararin sama.
- 24
Yowab ɗan Zeruhiya ya fara ƙirgan mutanen amma bai gama ba. Hasala ta sauko a kan Isra’ila saboda wannan ƙirge, ba a kuma shigar da adadin a littafin tarihin Sarki Dawuda ba.
- 25
Azmawet ɗan Adiyel shi ne mai lura da ɗakuna ajiyar fada.
- 26
Ezri ɗan Kelub shi ne mai lura da ma’aikatan gona waɗanda suke nome ƙasar.
- 27
Shimeyi mutumin Ramat shi ne mai lura da gonakin inabi.
- 28
Ba’al-Hanan mutumin Geder shi ne mai lura da itatuwan zaitun da na al’ul a gindin tuddan yamma.
- 29
Shitrai mutumin Sharon shi ne mai lura da garkuna masu kiwo a Sharon.
- 30
Obil mutumin Ishmayel shi ne mai lura da raƙuma.
- 31
Yaziz mutumin Hagiri shi ne mai lura da tumaki.
- 32
Yonatan, kawun Dawuda, shi ne mashawarci, mutum mai hangen nesa kuma marubuci.
- 33
Ahitofel shi ne mashawarcin sarki.
- 34
Yehohiyada ɗan Benahiya da Abiyatar ne suka gāji Ahitofel.