1 Chronicles 24
World English Bible (en) → Hausa Open Bible (Biblica) (ha)
- 1
Waɗannan su ne sassan ’ya’yan Haruna maza.
- 2
Amma Nadab da Abihu sun mutu kafin mahaifinsu, ba su kuma haifi ’ya’ya maza ba; saboda haka Eleyazar da Itamar suka yi hidimar firistoci.
- 3
Tare da taimakon Zadok zuriyar Eleyazar da Ahimelek wani zuriyar Itamar. Dawuda ya karkasa su zuwa ɓangarori don aikinsu bisa ga hidima.
- 4
Akwai ɗumbun shugabanni a cikin zuriyar Eleyazar fiye da zuriyar Itamar, aka kuma karkasa su haka, kawuna goma sha shida daga zuriyar Eleyazar da kuma kawuna iyalai takwas daga zuriyar Itamar.
- 5
Aka karkasa su babu sonkai ta wurin jifa ƙuri’a, gama akwai manyan ma’aikatan wuri mai tsarki da manyan ma’aikatan Allah a cikin zuriyar Eleyazar da Itamar.
- 6
Shemahiya ɗan Netanel, wani Balawe ne marubuci, ya rubuta sunayensu a gaban sarki da kuma a gaban manyan ma’aikata. Zadok firist, Ahimelek ɗan Abiyatar da kuma kawunan iyalan firistoci da na Lawiyawa, iyali guda daga Eleyazar, guda kuma daga Itamar.
- 7
Ƙuri’a ta farko ta faɗa a kan Yehoyarib,
- 8
na uku a kan Harim,
- 9
na biyar a kan Malkiya,
- 10
na bakwai a kan Hakkoz,
- 11
na tara a kan Yeshuwa,
- 12
na goma sha ɗaya a kan Eliyashib,
- 13
na goma sha uku a kan Huffa,
- 14
na goma sha biyar a kan Bilga,
- 15
na goma sha shida a kan Hezir,
- 16
na goma sha tara a kan Fetahahiya,
- 17
na ashirin da ɗaya wa Yakin,
- 18
na ashirin da uku wa Delahiya
- 19
Ga tsarin aikinsu na hidima sa’ad da suka shiga haikalin Ubangiji, bisa ga ƙa’idar da kakansu Haruna ya kafa, yadda Ubangiji, Allah na Isra’ila ya umarce shi.
- 20
Game da sauran zuriyar Lawi kuwa,
- 21
Game da Rehabiya kuwa, daga ’ya’yansa maza. Isshiya shi ne na fari.
- 22
Daga mutanen Izhar, Shelomot;
- 23
’Ya’yan Hebron maza su ne, Yeriya na fari, Amariya na biyu, Yahaziyel na uku da Yekameyam na huɗu.
- 24
Ɗan Uzziyel shi ne, Mika;
- 25
Ɗan’uwan Mika shi ne, Isshiya;
- 26
’Ya’yan Merari su ne, Mali da Mushi.
- 27
’Ya’yan Merari su ne,
- 28
Daga Mali, Eleyazar, wanda ba shi da ’ya’ya maza.
- 29
Daga Kish, ɗan Kish shi ne,
- 30
Kuma ’ya’yan Mushi maza su ne, Mali, Eder da Yerimot.
- 31
Suka kuma jifa ƙuri’a, kamar dai yadda ’yan’uwansu zuriyar Haruna suka yi, a gaban Sarki Dawuda da gaban Zadok, Ahimelek, da kuma a gaban kawunan iyalan firistoci da na Lawiyawa. Aka yi da iyalan wa daidai da iyalan ƙane.